Al Kurani (Quran in Hausa)
Musulunci shine addinin da mafiya yawan Hausawa suke bi. Kimanin kaso 90 ne na Hausawa suke bin addinin musulunci. Maanar Musulunci shine "Mika wuya ga kadaituwan Allah (SWT) cikin abubuwan da ya kebantu dasu, da mika wuya ga umarnin Allah Ubangijin talikai, tare da tsarkaka daga kafirci (sanya kishiya wa Allah) da kafirai." Allah (SWT) shi ya aiko Annabi Muhammadu (Yabo da Amincin Allah su Tabbata a gare shi) da Al Kurani Mai Girma. Yanzu haka, akwai fiye da Musulmai Biliyan Daya da Miliyan dubu dari biyar a fadin duniya.
Tarihin Addinin Musulunci
Asalin addini a duniya shi ne musulunci. Mutum na farko da Allah ya halitta, Annabi Adam (alaihis salam), ya rayu ne bisa tafarkin musulunci. Dukkanin manzanni tun daga Annabi Nuhu (alaihis salam), zuwa [[Annabi Ibrahim], da Annabi Musa, da Annabi Isa, alaihimus salam, musulmai ne ma su kadaita Allah. Sai dai gaba dayansu Allah ya aikosu ne zuwa ga alummominsu kadai. Annabi na karshe kuma cikamakin tsarin annabawa shi ne Annabi Muhammadu (yabo da amincin Allah su tabbata a gareshi). Allah ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) da sako zuwa ga daukacin alummar duniya, mutane da aljannu. An haifeshi a birnin Makkah da a yanzu ke kasar Saudi Arabia. Annabi Muhammadu (SAW), bakureishe ne, dan Abdullahi da Amina daga tsatson Annabi Ismaila (AS) dan Annabi Ibrahim (AS).